Idan ana son a raba talakawa da jin radadin matsalar sauyi yanayi to yakamata a inganta kiwon lafiyarsu
Yayin da akasarin talakawa ba su maida hankali ga abubuwan dake haddasa sauyin yanayi, kwararru su na gargadin cewa idan ba a yi wani abu yanzu da sauri ba, illar da zata yi zai rutsa da dukkan bil Adama.