Kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta Najeriya na kalubalantar gwamnatin tare da barazanar daukar mataki akan abin da ta ce rikon sakainar kashi da gwamnatin ke yi wa ilimi.
Hukumar kula da rayuwar dabbobi ta Majalisar Dinkin Duniya da masu kare hakkin dabbobi na Afirka, sun nuna damuwa ga yadda Jakuna ke matukar raguwa a duniya, saboda kashe su da a ke yi don samun nama da kuma amfani da fatar su wajen magani a kasar China.
Jami’an tsaron kan iyakar kasar Belarus sun ce, an tsare shugabar ‘yan adawar kasar Maria Kolesnikova da safiyar jiya Talata yayin da take kokarin tsallaka iyaka zuwa makwabciyar kasar Ukaraine.
Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya sallami hafsan hafsoshin sojin kasar ya kuma maye gurbinsa da tsohon kwamandan da aka kora a watan Maris.
Da alama kungiyoyin ‘yan ta’adda na ci gaba da kara karfin a wasu yankunan nahiyar Afirka, duk kuwa da kokarin da Amurka da kawayenta suke na ganin sun rage musu tasiri.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ziyarci wasu yankunan birnin Kenosha na jihar Wisconsin a jiya Talata, da aka lalata a tashin hankalin da ya faru makon da ya gabata.
Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar sakandare shida a lokacin da suke rubuta jarawabar karshe ta WAEC, a garin Udawa dake karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna.
Rundunar dakarun kawance na kasashen tafkin Chadi, (MNJTF a takaice) ta kubutar da wani ma’aikacin jinkai da ya kwashe watanni takwas a hannun kungiyar ISWAP wadda ta yi garkuwa da shi.
Wakilan babban taron jam’iyyar Republican na ta sauka a jihar North Carolina a wannan makon, inda saboda annobar coronavirus aka takaita adadin wadanda zasu halarci taron a zahiri da kuma wadanda za a gudanar ta yanar gizo.
Masana sun ce masu ikon fada a ji a kudancin Afrika na da gagarumar rawa da zasu taka a Mozambique domin dakile ayyukan ta’addanci na mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda dake arewacin kasar.
Dubban mutane sun yi cincirindo a babban birnin kasar Belarus a jiya Lahadi, suna kira ga shugaba Alexander Lukashenko ya sauka daga karagar mulki biyo bayan tarzoma da aka shiga kan zaben da ake takaddama a kai cikin cikkaken tsaron soja a birnin.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu matasa uku a garin Dan Musa da ke Jihar Katsina, bisa zargin aikata fyade da kisan kai.
Yawaitar kisan gilla tsakanin bangarorin dake gaba da juna a yankin Zuru na jihar Kebbi na ci gaba da haifar da zaman zullumi ga ilahirin al’ummar da ke masarautar Zuru.
Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da mutuwar wani farar fata dan kasar Lebanon, a hannun wasu ‘yan bidiga da suka yi garkuwa da shi ranar Litinin a jihar.
Majalisar dake kula da harkokin shige da ficen kasuwanci ta jiragen ruwan Najeriya, ‘Shippers Council’ ta koka game da karin harajin da ta yi zargin manyan kanfanonin jiragen ruwa na duniya su ka yi wa Najeriya.
Domin Kari