Suala yana cikin ‘yan jaridar nan da suka bankado wasu ayyukan cin hanci da rasahawa a hukumar kwallon kafa ta Ghana, lamarin da ya rutsa da shugaban hukumar Kwesi Nyantakyi. Ahmed Suala ya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan binciken fallasa kuma hakan yasa ya yi bakin jini a wurin wasu da lamarin ya shafa.
Wani dan majalisar dokoki mai wakiltan mazabar Assin North a jihar Tsakiyar Ghana, Kennedy Agyepong yana cikin wadanda suka nemi a kaiwa marigayin hari a duk inda aka same shi. Dan majalisar ya zargi Ahmed Suala da kamfanin Tiger Eye da shisshigi a cikin rayuwar mutane, lamarin da ya kai ga dan siyasar fitar da hoton Suala a kan telbijin, wanda ‘yan jaridar suka ce makaminsu ne hukokinsu da suka rufewa a duk inda suke.
Kisar Ahmed Hussein Suala ya janyo suka da zargi a kan dan siyasar saboda bayyana huskar dan jaridar. Mutane da dama ne suke zargin Kenney Agyepong cewa yana da masaniya a kan kisar, saboda alkawarin da ya dauka a baya a kan telbijin cewa zai biya duk wanda zai samu Ahmed Hussein Suala ya ci zarafinsa. Kuma tuni ‘yan sanda sun gayyaci dan majalisar don yi masa tambayoyi.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya jajantawa iyalan marigayin kuma da kakkausar murya ya yi tir da wannan danyen aikin kuma ya kira ma’aikatar ‘yan sandan Ghana ta gaggauta kamo wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Ita ma kungiyar ‘yan jarida ta kasar Ghana ta bakin shugabanta Affail Mooney, ta yi Allah wadai da wannan kisar ta kuma kwatanta kisar da babban bala’I ga aikin jarida a Ghana. Anas Aremeyaw Anas shugaban kamfanin Tiger Eye PI da marigayin ke aiki karkashinsa, ya lashi takobi cewa wannan kisar da zata sa su yi shuru ba, zasu ci gaba da aiki.
‘Yan jarida a Ghana sun bayyana kaduwarsu ga wannan danyen aiki da ba a saba gani a cikin kasar kana sun yi kira ga hukumomi su tashi tsaye su kare ‘yan jarida. Haka zalika ‘yan Ghana sun yi amfani da shafukan sada zumunta wurin bayyana alhininsu ga wannan kisar.
Ga ra’ayoyin wasu ‘yan jarida a Ghana da wakilinmu Ridwan Muktar Abbas ya tattaro mana:
Facebook Forum