Real Madrid ta doke Paris Saint Germain da ci 3-1 a zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA.
Dan wasan Real Madrid Karim Benzema ne ya zura kwallayen duka uku a ragar PSG a minti na 61, 76 da kuma 78.
Kididdiga ta nuna cewa cikin minti 16 Benzema ya zura duka kwallayen.
Madrid, wacce ta karbi bakuncin wasan ce ta fara zura kwallon farko ta hannun Kylian Mbappe a minti na 39.
Hakan na nufin karawar bangarorin biyu ta kare da jimillar ci 3-2, wato Madrid ta yi nasara akan PSG wacce yanzu ta fita a gasar kenan.
A karawar farko PSG ta lallasa Real Madrid da ci 1-0 a Paris.
Wannan nasara da Madrid ta samu na zuwa ne yayin da Mbappe ke ci gaba da hankoron ganin ya koma bugawa kungiyar wacce ke Sifaniya.
A watan Yulin bana kwantiragin Mbappe zai kare da PSG, ko da yake, rahotannni na nuni da cewa kungiyar ta PSG tana fatan zai kara tsawaita zamansa a Paris.