Tawagar shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari tare da hadin gwiwar hukumar kai agajin gaggawa ta NEMA, sun tallafawa mutane 76 da harin bam ya rutsa da su makon da ya gabata a kasuwar Madagali, da kuma ke samun kulawa a Asibitin Michika dake jahar Adamawa.
Gwamnatin jahar Adamawa ta raba Taraktocin noma sama da ‘dari ga kananan hukumomin jahar 21, domin bukasa harkar noma a jahar.
Tagwayen bama bamai sun tashi a lokacin da ake hada hadar cin kasuwa a garin Madagali dake jahar Adamawa, wanda kawo yanzu babu masaniyar ko mutane nawa ne suka rasa rayukansu.
Yayin da dakarun Najeriya ke ci gaba da kwato dukkanin yankunan dake hannun mayakan Boko Haram a jihohin Adamawa, Borno da kuma jihar Yobe, yanzu haka hukumar samar da wutar lantarki ta fara samar da wuta a wasu yankunan da aka kwato.
Wasu yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu da yanzu haka ke samun mafaka a jihar Taraba sun soma kokawa da cewa an manta dasu, inda suke neman komawa jiharsu ta Borno.
Matsalar rashin kudi da kuma tsadar rayuwa ta soma tilastawa wasu magidanta guduwa suna barin iyalansu, batun da yanzu ke kara barazana ga rayuwar ma’aurata.
Wasu mata da suka rasa mazajensu sun koka kan cewa yanzu haka suna cikin wani halin ban tausayi, sakamakon matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita, wanda don haka suka mika kokon bararsu da ake tunawa dasu.
Baya ga rayuka, wani batu da rikicin Boko Haram ya shafa matuka shine harkar noma, sakamakon raba dubban manoma da gonaki da kuma gidaje, lamarin dake kara barazana ga harkar samar da abinci.
Yayin da yan gudun hijira a jihar Taraba ke ci gaba da kokawa kan rashin samun kayayyakin tallafi da gwamnatin tarayya ta turo jihar, biyo bayan takaddamar data kaure a tsakanin gwamnan jihar da kuma Ministan harkokin mata.
Yanzu haka wata takaddama ta kaure a tsakanin gwamnan jihar Taraba Akitet Darius Dickson Isiyaku, da kuma Ministan harkokin mata da walwalar jama’a Sanata Aisha Jummai Alhassan Maman Taraba, game da rabon kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta turo jihar don arabawa yan gudun hijira, inda gwamnatin jihar ta hana ministan raba kayayyakin.
Yayin da ake fama da matsalar satar shanu da kuma garkuwa da mutane a jihar Taraba, matsalar da yanzu ke neman hana jama’a barci a jihar, shugabanin Fulani makiyaya sun gudanar da wani taron nemo bakin zaren magance wadannan matsaloli da akan dangantawa da makiyaya.
A wani sabon yunkuri na magance matsalar cunkuson ababen hawa dake barazana ga harkar tsaro a jihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya na cewa mahukunta a jihar sun kaddamar da dokar hana kasa kaya da kuma ajiye a baben hawa a bakin titi.
Yayin da uwar jam’iyar APC a Najeriya ke haramar karbar wasu kusohin jam’iyun adawa a jihar Adamawa,yanzu haka wata sabuwa ce ta kunno inda wasu yayan jam’iyar yan bangaren gwamnan jihar ke cewa ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa.
A wani yunkuri na ganin an samu dawwamamman zaman lafiya a jihar Adamawa, manyan sarakunan jihar sun gana da gwamnan jihar inda suka tabo hanyoyin samun zaman lafiya.
Mallam Garba Shehu yayi watsi da batun yin bi-ta-da-kulli musamman ma shugabannin majalisar dattawa, yana mai cewa atoni-janar yana da hurumin gurfanar da duk wanda ake tuhuma a gaban kotu.
Muhammadu Buhari na yabawa 'yan Najeriya game da fatan alheri da ake masa
Hadakar kungiyar malamai ta Najeriya, NUT, ta nuna fushinta game da rashin biyan albashi na malaman makarantun firamare a jihar na tsawon watanni, lamarin da yasa malaman fusata da rufe makarantu, yanayin da yasa dalibai komawa gida.
Rahotanni daga jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya na cewa an samu asarar rayuka masu yawa a wani sabon rikici da ya sake barkewa a garin Tella,cikin karamar hukumar Gassol