Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirya Addu'oi Na Masamman Ga Shugaba Muhammad Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari na yabawa 'yan Najeriya game da fatan alheri da ake masa

Yanzu haka a Najeriya,kungiyoyin addini dana shugabanin al’umma na cigaba da shirya addu’o’I na musamman ga shugaban Najeriyan,yayin da a bangare guda kuma wasu yan kasar ke bayyana mabanbantan ra’ayi game da salon gwamnatin APC.

Shugaba Buhari dai ya tafi hutu zuwa kasar Ingila ,biyo bayan tsanantan ciwon kunnensa,kuma ba kamar dai a baya ba,a wannan karon ba’a boyewa yan Najeriya rashin lafiyan shugaban kasar ba,da hakan ya magance cecekucen da ka iya faruwa.

Shi dai shugaban Najeriyan Muhammadu Buhari, na cigaba da hutu da kuma murmurewa daga jinyan ciwon kunnen da yake fama da shi,yanzu haka kungiyoyi da kuma shugabanin al’umma na cigaba da shirya addu’o’I na musamman ga shugaban Najeriyan,yayin da a bangare guda kuma wasu yan kasar ke bayyana mabanbantan ra’ayi game da salon gwamnatin APC.

Kuma alfarmar wannan wata na azumin Ramadan nema yasa kungiyar Izala a Najeriya gudanar da addu’o’I domin lafiyar shugaba Buhari,da kuma samun cigaba a Najeriya.

Ana yin addu’o’in ne a fadin Najeriya,kamar yadda shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi bayani.

Haka nan kuma,kamar kungiyoyin addini,suma dai gwamnonin jihohi,sun soma yin kiran da ayi addu’o’I ga shugaba Buhari, inda gwamnan jihar Sen. Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla ya umarci al’umman jihar da su gudanar da addu’o’I na musamman.

Wannan na zuwa ne,yayin da magoya bayan jam’iyar APC,ke maida martani ga masu zargin cewa Buhari na tafiyar hawainiya.Sardaunan Jimeta Muhammad Haladu Dan Kwai na masu ganin gazawar yan Najeriya.

To sai dai kuma duk,da halin da ake ciki a yanzu,Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, na yabawa 'yan Najeriya game da fatan alheri da ake masa.

Hon.Ibrahim Bapetel Hassan, hadimin shugaban kasan kan ayyuka da tsare tsare,ya ce ba kamar dai a baya ba,a wannan karon ba’a boyewa yan Najeriya rashin lafiyan shugaban kasar ba,da hakan ya magance ce ce ku cen da ka iya faruwa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG