Ma’abota sauraron Sashen Hausa na Muryar Amurka na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su kan cikar sashen shekaru 45 da fara aiki.
Sai dai a wannan shekarar, lamarin ya sha banban da yadda aka saba saboda farashin man fetur ya ninninka kudinsa: hakan ya haddasa tsadar kudin mota ninkin-ba-ninkin.
Wasu mata ‘yan jarida a arewacin Najeriya sun kaddamar da wani zaure da zai zama na hadin kai don karfafawa mata gwiwa domin yin aikin da samun nasarar gogaiya da sauran ‘yan jarida na kasa.
Shugaban Hukumar NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bitar matakan da hukumar ke dauka don tunkarar aikin hajin da ke tafe na shekarar 2024.
Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta kaddamar da kwamitin tantance kamfanonin jirgin saman fasinja da na dakon kaya don aikin hajjin 2024.
Kamfanin tsare-tsare da bincika na Duke tare da hadin gwiwar Gidauniyar tattalin arziki na Musulunci a Africa sun gudanar da taron na musamman don tattauna hanyar za’a kawo sabbin dabarun duba marasa lafiya a matakin farko tare da basu magani cikin sauki ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Tun bayan cire tallafin man fetur a Najeriya al’ummar kasar ke kokawa kan yadda kayan abinci ya yi tashin gwaron zabi a kasar da hakan yasa mutane da dama musamman masu karamin karfi basa iya cin abinci sau uku a rana.
Masana harkar hakowa da sayyar da man fetur a Najeriya sun baiyana cewa har yanzu zabi mafi muhimmanci wajen samun saukin farashin fetur shi ne kafa kananan matatu masu saukin sarrafawa.
Domin Kari