A bisa al'ada, duk shekara, mabiya addinin Kirista da musamman ma'aikatan gwamnati kan yi dandazo a tashoshin mota, don tafiya garuruwansu na asali don gudanar da bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Sai dai a wannan shekarar lamarin ya sha banban da yadda aka saba saboda farashin man fetur ya ninninka kudinsa; hakan ya haddasa tsadar kudin mota ninkin-ba-ninkin.
'Yan kwanaki gabannin bikin Kirsimeti da sabuwar shekarar 2024 miladiyya, tashohin mota da ke birnin tarayya Abuja ba su yi cikar da aka saba gani ba a baya ba, sakamakon cire tallafin man fetur da ya haddasa tsadar man, don haka yin irin wannan tafiya sai dai karfin hali ko idan ya zama dole.
Wani direba a tashar Maraba mai suna Garba Abdullahi, ya ce sun shafe shekara da shekaru suna jan mota, amma ba su taba shiga irin halin da ake ciki a yanzu ba.
Ita ma Rukayya matafiya ce a daidai irin wannan lokaci na kowace shekara, ta ce da ma kudin motan kan karu amma na wannan karon abin ya wuce misali.
Da yake karin bayani Ministan yada labarai na Najeriya, Muhammad Idris, ya ce ma’abota kamfanonin sufuri 5 ne kawai gwamnati ta dauka da biyansu tallafin kashi 50 don amfanin jama’a.
Ministan ya amsa tambayar ganin karancin kamfanonin, yana mai cewa, idan an duba za’a iya kara wasu kuma sam ba za’a saurari shawarar bankin duniya na sayar da litar man fetur kan naira 750 ba.
A wannan makon, rahotannin sun ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta sanar da wani shiri na zarftare kudaden mota ga masu tafiye-tafiye don a rage musu radadin tsadar kudin mota.
Kazalika gwamnatin ta saka jirgin kasa kyauta ga matafiya a kasar.
Wannan shiri ya fara aiki ne daga wannan lokaci har zuwa 4 ga watan Janairu.
Saurari cikakke rahoton Hauwa Umar:
Dandalin Mu Tattauna