Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Doctors Without Borders Ta Ce Musulman Rohingya 6700 Aka Kashe


Kungiyar Likitocin Kasa Da kasa ta Doctors Without Borders, ta ce akalla Musulmi ‘yan kabilar Rohingya dubu shida-da-dari-bakwai aka kashe a watan farkon samamen da dakarun kasar Myanmar suka kai akan ‘yan tawayen Rohingya.
Kungiya mai ba da tallafi wacce ke Geneva, wacce kuma aka fi sani da “Medecins Sans Frontieres”, ko kuma MSF a takaice, a yau Alhamis ta ce ta kai ga wannan kididdigar ne, bayan da ta gudanar da wani bincike akan ‘yan kabilar ta Rohingya da dama da ke neman mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijra a Bangladesh.
Daga cikin wadanda suka mutu kamar yadda kididdigar ta nuna, har da yara kanana 730 da shekarunsu suka gaza biyar.
Ana dai zargin sojojin kasar ta Myanmar da kaddamar da wannan samame ne akan kauyukan ‘yan kabilar ta Rohingya a jihar Rakhine da ke arewa maso yammacin kasar a watan Agusta.
Mummunan samamen, ya biyo bayan wasu hare-hare da masu fafutuka ‘yan kabilar ta Rohingya suka kai akan wasu ofisoshin ‘yan sandan kasar.
Wannan samame ya haifar da tserewar ‘yan Rohingya dubu dari shida zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da Myanmar.
‘Yan gudun hijrar sun fadawa kungiyoyin kare hakkin bil adama labarin ire-iren cin mutuncin da aka musu da suka hada da kisan kai, fyade da kuma kona baki dayan kauyukansu.
Darekatan kungiyar ta MSF, Sidney Wong, ta ce sakamakon binciken na su abu ne “mai gigitarwa” idan aka yi la’akkari da adadin mutanen da suka ba da labarin yadda aka kashe masu ‘yan uwa da kuma irin mummanar hanyar da aka kashe su, ko kuma aka jikkata su.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG