A yau Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya yi watsi da zargin cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na bara.
Ya kuma kara da cewa abokanan hamayyar Shugaba Trump ne suke yada wannan zargi, domin su haramta shugabancinsa.
Yayin da yake magana a taron manema labarai na gaggawa da yake yi a duk shekara, Putin ya yi fatan dangantakar Amurka da Rasha za ta samu daidaito.
Hukumomin tattara bayanan sirrin Amurka dai sun yi amannar cewa shugaba Putin ya ba da umurnin a yi shisshigi a kuri’un zaben na Amurkan, inda ya nuna fifiko akan Trump domin ya kada tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.
Shi ma dai Trump ya yi ta nanata cewa, gangamin yakin neman zabensa bai hada kai da Rasha ba.
Shugaba Putin har ila yau, ya nuna damuwarsa kan shirin Amurka na janyewa daga wata yarjejeniya ta dakile yaduwar makamai da aka kulla, yana mai cewa Rasha za ta ci gaba da mutunta matsayar da aka cimma.
Ya kuma kara da cewa dakarun Rasha za su ingantu kamar yadda ya kamata, ba tare da Rashan ta shiga rigerigen mallakar makamai da Amurka ba.
Facebook Forum