Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana neman tallafin dala miliyan dubu biyu da miliyan dari bakwai, domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Sudan ta Kudu sama da miliyan biyu da ke bukatar agaji.
‘Yan gudun hijirar a cewar hukumar, na zaune a wani mawuyacin hali a wasu kasashe shida, da ke makwabtaka da kasar, yayin da kudaden da ake amfani da su wajen tallafa musu ke gab da karewa.
Matsalar ‘yan gudun hijirar Sudan ta Kudu, ita ce mafi girma a Nahiyar Afirka, wacce kuma ke samun mafi kankantar kudaden tallafi.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta bayyana cewa, kashi 38 kadai cikin 100 na yekuwar neman taimakon dala miliyan $1.4 da ta nema aka samu.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa, zafin rikicin kasar ya kwanta, saboda yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a watan Satumba, bayan da kasar ta kwashe shekaru biyar tana fama da yakin basasa.
Facebook Forum