Muryar Amurka ta tattauna da wani mai fafutuka da sharhi a Najeriya, Nastura Ashir Sharif ta Skype, inda muka ji ra’ayin shi a game da tallafin rage radadin a wannan lokaci.
Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudurin doka da za ta haramta zargin mutane da maita. Idan kudurin ya zama doka, zai tilasta rufe sansanonin da mutanen da ake zarga da maita suke zuwa neman mafaka don kar a halaka su.
A jihar Bornon Najeriya mutane da dama na korafin rashin yin adalci wajen rabon tallafi, inda wasu kuma ke cewa labarin ana rabon kayan abinci kawai suke ji, amma bai kai garesu ba.
A game da girgizar kasar a Morocco, Muryar Amurka ta tattauna da Farfesa Adnan Abdulhamid na Jami’ar Bayero dake Kano inda ya yi mana karin haske akan wasu dalilai da suka sa girgizar kasar a Morocco ta yi muni sosai.
Mutane da dama a sassan Najeriya su na sukar wannan shiri na raba tallafin rage radadi, inda wasu ke cewa akwai cuwa-cuwa a ciki, da siyasa, da jinkiri, sannan a wasu wuraren abin da ake ba mutane bai taka kara ya karya ba.
Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudurin doka da za ta haramta zargin mutane da maita; Mutane da dama a sassan Najeriya su na sukar shirin gwamnatin kasar na raba tallafin rage radadin rayuwa, da wasu rahotanni
WHO ta ce rashin abinci mai gina jiki, cuttuka masu yaduwa daga mutum zuwa wani, cututtuka masu tsanani, jinin al’ada mai zuba da yawa, matsaloli a yayin da mace take da ciki da kuma cututtuka da ake gadonsu suna daga cikin abubuwan da ke kai ga kamuwa da anemia.
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta ware sama da Naira miliyan 800 don gudanar da auren mutane 1,800 lokaci daya a karkashin wani shirinta na aurar da zaurawa; Wani matashi injiniya a Maiduguri ya na kera keke mai amfani da lantarki don baiwa mutane samun saukin zirga-zirga, da wasu rahotanni
Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya RIFAN, ta ce sama da masana’antun shinkafa 50 a jihar Kano aka rufe saboda karancin shinkafa a fadin kasa; Wasu manoma mata da miji ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka suna amfani da fasaharsu wajen inganta sana’arsu ta noma a jihar Maryland, da wasu rahotanni
A wani mataki na tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, gwamnati ta raba ababen hawa ga jami’an tsaro da ‘yan sa-kai a jihar.
Tattala muhalli ta hanyar dasa bishiyoyi da kula da shuke-shuke, shi ne abin da ya zama jigo a shagulgulan bikin ranar matasa ta duniya a jihar Filaton Najeriya, wanda aka yi a ranar 12 ga watan Agustan 2023.
Kowace shekara, ’yan kungiyar Zumunta suna haduwa a wuri guda domin sada zumunta da kuma duba yiwuwar yadda zasu taimaka wa juna da kuma yadda zasu bada nasu gudunmawa wajen cigaban Najeriya. Sannan yin hakan yana taimaka wa yaran da suke Haifa wajen fahimtar al’adu da mahimmancin hadin kai.
Shugaban Ghana Nana Akufo Addo, ya sanya hannu kan kudirin dokar da Majalisar Dattawan Ghana ta amince na soke hukuncin kisa; Shugabannin mata na Fulani sun ce mata za su iya taka muhimmiyar rawa wajen rage takun saka tsakanin manoma da makiyaya, da wasu rahotanni
Glacoma shike kan gaba wajen haifar da makantar da idanu basa a sake gani na (dindindin), sannan itace abu na biyu dake haifar da makanta.
Gwamnatin Kenya na samar da matsugunai ga wadanda suka tsira daga safarar mutane; Ficewar Rasha daga yarjejeniyar fitar da Hatsi ta Bahar Maliya na shafar kokarin Najeriya na dogaro da kai, da wasu rahotanni
A Nijar, inda aka samu juyin mulki sannan aka kakaba wa kasar jerin takunkumai, ayyukan kungiyoyin jinkai ya ragu sossai, lamarin da ya jefa al’ummomin da suke ba su tallafi cikin takaici.
Karancin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya na shafar hanyoyin samun kulawar mutane, da ingancin kulawar da suke samu, da kuma yawan mutanen dake mutuwa sakamakon cututtuka a nahiyar.
Akan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri, mun kuma duba taron gaggawa da Kungiyar ECOWAS ta yi a Abuja, Najeriya, da wasu rahotanni.
Halin matsin tattalin arziki a Najeriya sakamakon cire tallafin man fetur ya sa hukumomin yin kokarin bunkasa amfani da wasu hanyoyin makamashi da ba na fetur ba, abin da ya hada da canza injuna zuwa masu aiki da iskar gas da fadada tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki, da wasu rahotanni
Kwararru sun ce ana samun karuwar mutane masu kananan shekaru tattare da cutar bugun jini a fadin duniya sannan wasu dalilai da suke haifar da wannan yanayi sun hada da kiba mara kima, hawan jini da kuma cutar sukari wato diabetes.
Domin Kari