Najeriya ta yi kira ga MDD da ta bayar da fifiko ga neman yafewa kasashe masu tasowa basussuka ta kuma bukaci a ba ta kujera ta dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar; Mutanen da ambaliya ta lalatawa gidaje a Maiduguri suna zargin hukumomi da tashisu daga gine-ginen gwamnati, da wasu rahotanni
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Trump mai shekaru 78, wanda ke neman sabon wa’adin mulki a Fadar White House, ya yi ikirarin cewa Iran na barazana da rayuwarsa.
'Yan sandan jihar Zamfara sun yi faretin wani Jam'in Civil Defense da ke yi wa 'yan bindiga safarar makamai, Likitan jabu, da matan manyan 'yan bindiga cikin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka
Rikicin kabilanci tsakanin Fulani da kabilun Gomon ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
Harin an kai shi ne a kan dakarun sa kai na RSF, a wani mataki na farmakin soja mafi girma tun bayan barkewar rikicin.
Ya kara da cewa "Bai kamata a ci gaba da wannan haukar ba. Daukacin duniya na da alhaki akan abin da ke faruwa ga mutanen mu a Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana damuwarsa ga hafsan hafsoshin sojin Sudan a game da yadda ricikin kasar yake dada ruruwa, yayin da suka gana a wani taron manyan jakadu a birnin New York a ranar Laraba.
Al'umar jihar Zamfara sun fara kokawa akan ce-ce ku-cen da ake yi tsakanin gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da karamin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Bello Muhammad Matawalle.
Kakakin majalisa Mike Johnson kuma dan jam’iyyar Republican ya ayyana wannan matakin a matsayin, “wani abin da ya zama wajibi da babu makawa.”
Domin Kari