Jami’an lafiyar Falasdinu sun ce hare haren saman da Isra’ila ta kai cikin dare a Gaza ya hallaka mutane 12. Sannan, ‘yan sandan Isra’ila sun kama wasu mutane 3 da suke zargi da cinna wuta a wani gida mallakin Firan ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu a birnin Caesarea dake gabar teku.
Hukumomin Isra'ila sun ce Netanyahu da iyalen sa basa gidan a lokacin da aka samu tashin gobara har sau 2 cikin dare, sannan babu wanda yayi rauni. Jami’a sun dora alhakin faruwar wannan lamarin akan masu sukar siyasar Netanyahu a cikin gida.
A Lebanon kuma, jiragen yakin Isra’ila sun yi ta luguden wuta a garuruwan dake yankin kudancin Beirut da sanyin safiyar yau Lahadi bayan da sojoji suka gargadi mutane su kaurace daga sauran gidaje akalla 7.
Akwai ‘yan Kungiyar mayakan Hezbollah da dama a yankin sannan farmakin na zuwa ne a sa’adda jami’ai suke shawarar amincewa da tayin tsagaita wuta da Amurka ta mata
Dandalin Mu Tattauna