Sabuwar muzaharar ‘yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Elzakzaky a Zuba jihar Neja dab da Abuja, ta jawo daukar matakin dakilewa daga jami'an soja, inda hakan ya haddasa rasa rayuka.
‘Yan Shi’an dai da ke muzahara da ambata kamfen din neman a sako shugaban Ibrahim Elzakzaky wanda ke hannun jami’an tsaro tun Disambar 2015, sun gamu da sojojin a daidai babbar gadar marabar tafiya Abuja daga yankin Zuba.
Daya daga cikin masu muzaharar, Muhammad Ibrahim Gamawa, ya tabbatar da mutum 6 sun rasa ran su, inda biyu kuma ke cikin mawuyacin yanayi.
"Duk wadanda su ka mutu 'yan maza ne," inji Ibrahim Gamawa, wanda ya kara da cewa da alamun ya tsira daga mutuwa ne don bai sanya bakaken kaya ba kuma in irin hakan ya faru wasu daga cikin su kan yi hikimar kauda-bara ta hanyar kwantawa don kaucewa gamuwa da albarushi.
A halin yanzu dai ba bayani daga hukumomin tsaro kan lamarin da ya zama ba sabon abu ba tsakanin ‘yan Shi’an da kuma jami’an tsaro da ke cewa ‘yan Shi’an ba sa neman izini kafin su yi zanga-zangar.
Facebook Forum