Kamar yadda ganau suka tabbatar, wasu yan ina da kisa ne, suka yi shigar burtu zuwa dab da kasuwar ta mararrabar Kunini, kuma kafin kace kwabo sai suka soma bude wuta. Nan take mutum biyu suka rasu, baya ga wadanda aka garzaya da su asibiti cikin gaggawa.
Wannan dai ita ce sabuwar kasuwar dabbobin da aka bude a watan jiya, kuma tuni ta soma habaka, biyo bayan mutuwar babbar kasuwar Mayo Lope da tashe tashen hankula suka daidaita.
Da take tabbatar da wannan hari da akan kasuwar mararrabar kuninin, rundunar yan sandan jahar Taraba, ta bakin kakakin ta ASP David Misal ta ce kawo yanzu babu wanda aka kama amma tuni har an soma bincike.
Ba wannan ba ne karon farko na kai hare-hare a kasuwannin jahar, domin ko yan makwannin nan an kai wasu hare haren a wasu manyan kasuwanni jihar da suka hada da kasuwar iware, lamarin da yanzu haka ke bukatar daukan mataki domin kada lamarin ya durkusar da harkar kasuwanci a jihar Taraba.
Facebook Forum