FARANSA: daliban makarantar sakandaren kasar Farasan sun tada wuta a gaban marantar su yau Talata a yayinda suka yi gangami a wurare dabam dabam a matsayin bangaren wata zanga zanga da ake yi a kasar.
Shaharraren Dan tseren kasar Kenya Eliud Kipchoge ya karbi lambar yabon hukumar wasan tseren kasa-da-kasa jiya talata a matsayin gwarzon namiji a fannin tseren da ya shekarar 2018
Nigeria: Wasu masu sha’awar tseren keke, sun shirya gasar tsere a Legas, da zimmar bunkasa wasan tseren keke a Najeriya, wacce ta fi maida hankali kan wasan kwallon kafa.
US: Shugaba Donald Trump da mai dakinsa, Melania, sun kai ziyarar ban girma a inda majalisar dokoki akwatin dake dauke da gawar tsohon shugaba Goerge H.W. da ya rasu.
Dubban jama’a sun yi zanga-zangar kin amince da zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka yi jiya Lahadi a Tbilisi dake Georgia, suna imanin an tafka magudi a zaben.
Mexico: Bakin hauren da suka fito daga yankin tsakiyar Amurka, sun nufi wani matsuguni na biyu a Tijuana a daren jiya Alhamis, yayin da ‘yan gudun hijra dubu shida ke tsaye a kan iyaka Amurka, inda suke jiran dama ta samu domin su shiga.
Uganda: An kirkiri wata manhaja, saboda masu fama da cutar AIDS da sauran cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i, su rika samun bayanai kan lafiyarsu. Nabembezi ‘yar shekaru 23 ce ta kirkiri manhajar, wacce ake kira “Ask without Shame” wato ka tambaya ba tare da ka ji kunya ba.
A Najeriya,dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya fara yakin neman zabe, a kokarin da yake yi na ka da shugaba Muhammadu Buhari da ke neman wa’adi na biyu.
‘Yar takarar jam'iyyar republican Cindy Hyde Smith ta lashe zaben majalisar dattawa a jihar Mississipi. Yanzu ‘yan Republican na da kujeru 53 cikin 100 na majalisar.
Shugaban Masar Abdel Fatal Al Sisi, ya tarbi Yarima Muhammad Bin Salman mai jiran gado a lokacin da ya isa binrin Alkahira a ranar Litinin. Wannan it ace ziyararsa ta farko, tun bayan kisan dan jarida Jamal Khashoggi da ta janyo suka daga sassan Duniya.
Domin Kari