Wannan shine karo na biyar da shugaba Buhari ke samun gagarumin rinjaye a jihar Kano tun bayan da ya fara takarar shugabancin Najeriya a shekara ta 2003.
Sai dai duk da haka da dama mutanen Kano sun koka wajen samun ababubuwan da zasu habbaka harkokin tattalin arziki ta bangaren noma da ci gaban masana’antu, da kasuwanci da jihar ta shahara akan su.
Wasu matasa sun bayyana mamakin su akan yadda shugaban ya mayar da Kano saniyar ware a cikin shekaru 4 na gwamnatin sa.
Suma dai dattawan jihar sun tabbatar da yanayin rashin raba kayayyakin habbaka rayuwar Jama’a daga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari cikin shekaru 4 baya, musamman idan aka kwatanta da rawar da take takawa wajen nasarar shugaban a fagen zabe.
A yayin walimar cin zabe da magoya baya suka yi, shugaban kwamitin yakin neman zabe na shugaba Buhari a jihar Kano. Alhaji Sabo Nanono yayi Karin haske game da lafazin da yayi cewa, yanzu kanawa suke bin shugaba Buhari bashi.
Shi kuwa Janar Bashir Salhi Magashi cewa yayi, sun daura damarar ganin Kano ta rabauta da ayyukan gwamnatin Buhari a wannan Karo.
Facebook Forum