A Puerto Rico, gwamna Ricardo Rossello zai yi murabus daga mukaminsa bayan kwanakin da aka kwashe ana zanga zanga akan titunan yankin don neman yayi murabus saboda wata takaddamar rubuce rubuce da rashawa a gwamnatinsa.
Babban hafsan sojan kasar Sudan na daya daga cikin mutane da yawa da aka kama suna shirin yin juyin mulki, a cewar sojojin kasar jiya Laraba. Jim kadan bayan haka, Rahotanni sun bayyana cewa an kama akalla manyan sojojin kasar kusan 12 da ‘yan bindiga saboda kitsa juyin mulkin.
Sai kuma a kasar Uganda inda shahararen mawakin nan da ya zama shugaban ‘yan adawa, Bobi Wine, ya ayyana shirinsa na karawa da dadadden shugaban kasa Yoweri Museveni a zaben 2021.
Bari mu fara daga yankin Afrika inda yawan neman zinari da ake yi a kasuwanni yake yin illa ga muhallin yankunan Afirka, lamarin da yake kai wa har ga yankin Asiya da Kudancin Amurka.
Ga labarin wani mawaki zabaya dan kasar Malawi dake yaki da dabi’ar kyamatar zabayoyi da kuma camfe-camfe akansu a kasar. Yanzu haka yana shirin fitar da sabbin wakokinsa cikin wata mai zuwa bayan ya hadu da wani dan kasar Sweden da ya taimakamasa.
A kasar Somliya akalla murtane 17 ne aka kashe kana wasu 28 suka jikkata bayan harin da da wata mota dauke bam ta yi a Mogadisho babban birnin kasar. Kungiayr Alshabab ta dauki alhakin wanan harin.
Fira ministan Ingila Theresa May ke ganawa ta gagawa tare minsitan tsaro da kuma wasu jami’a domin tattaunawa akan yadda za’a ciyo kan kama jirgin kasar da kasar Iran ta yi a yinkin Hormuz.
Hukumar lafiya ta duniya ta WHO ta ce barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo babban kalubalen lafiyar al’umma ne da ya baci wanda kasashen duniya suka damu da shi.
A Amurka, kungiyoyin fararen hulla da dama sun gabatar da kokensu na dakile sabuwar dokar gwamnatin Trump akan neman mafaka a Amurka na wani dan lokaci, wadda ta fara aiki shekaranjiya Talata.
TASKAR VOA: A Cikin Shirin Taskar VOA Na Wannan Mako Za Kuga Yadda Kungiyar Hadin Kan Afrika Da Ake Kira AU Ta Kamalla Wani Babban Taro A Jamhuriyar Nijer
Gwamnatin kasar Turkiyya ta karbi rukunin makaman masu linzame na kariya kirar S400 a yau juma’a daga kasar Rasha bayanda kasar Amurka ta gargadi Turkiyar akan kada ta karbi makaman ko kuma ta fuskanci horo daga Amurka.
Bari mu fara daga kasar Sudan, inda Janal Gamal Omar ya bada sanarwa cewa akalla manyan sojoji 16 tare shugabansu ne aka kama bayanda suka yi yunkurin juyin mulki a jiya Alhamis. Dakarun kasar na ci gaba da neman sauran wadanda ke da hannu akan lamarin.
Najeriya: A Ranar Talata, magoya bayan shugaban ‘yan Shi'a da aka tsare, sun yi arangama da jami'an tsaro a kusa da majalisar dokokin Najeriya a wani sabon rikicin da ya barke tsakanin ‘ya’yan kungiyar da hukumomin kasar.
A wata ziyara da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya kawo birnin Washington DC, muryar Amurka ta sami damar yin hira da shi inda har suka tabo batun tsaro a Najeriya
Birtaniya: Jakadan Birtaniya a Amurka, Kim Darroch (DAROK) ya yi murabus, yana mai cewa "ba zai yi wu ba" ya ci gaba da aikinsa ba bayan da aka kwarmata bayanan diflomasiyyan da suka soki shugaban Amurka Donald Trump.
Amina Muhammad ta nuna damuwarta game da yadda rigingimu ke shafuwar ayyukan tallafawa mata da yara a wasu kasashen Afrika,ta ko bayyana haka ne a taron kungiyar Tarayyar Afrika da ta halarta a birnin Yamai na Jamhuriyyar Nijar.
Domin Kari