Wata tawagar 'yan jam’iyyar adawa ta Moden Lumana a Jamhuriyar Nijar, wacce shugaban ‘yan adawa Hama Amadou da ke gudun hijra ke jagoranta, tayi wani taro a birnin New York da ke nan Amurka, inda magoya bayan jam'iyyar mazauna Amurka suka halarci taron.
An dai yi wannan taron ne a cibiyar raya al'adun bakar fata da ke birnin na New York, inda aka kafa sabon reshen jam’iyyar a nan Amurka, wadanda suka maye gurbin tsofafin zababbun mambobin jam'iyyar, wadanda suka kammala wa’adinsu.
‘Yan kasar Nijar da dama magoya bayan wannan jam’iyyar sun nuna kauna, da haddin kai ga junansu lokacin da aka gudanar da wata liyafa tare da raye-raye da kade-kade.
A lokacin da yake jawabi shugaban da ke kulla da wannan taro ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da daukacin’yan Nijar su hada kansu.
Bayan haka tsohon shugaban jam’iyyar mai barin gado Alhaji Tayabu Abdullahi, ya mika na shi sakon inda yace shekaru hudu kenan da ya jagoranci reshen jam'iyyar Modem Lumana a Amurka, kuma lokaci ya kai su ba wasu damar jan ragamar wannan jam'iyyar. Ya kara kiran hadin kan jama'a baki daya na gida Nijar da kuma nan Amurka.
Ita kuwa Hajia Hawa Issaka wadda ta wakilci sabon shugaban wannan jam’iyyar reshen da ke nan Amurka, ta yi karin haske akan dalilin hada wannan taro inda ta ce; wannan rana ce ta nada sababbin shugabannin jam'iyyar su ta adawa reshen kasar Amurka.
Suna mika kiran su ga shugaba Isufu Muhamadu, da ya bar 'yan adawa suma su fadi albarcin bakunan su, akan yadda abubuwa ke gudana a kasar, suna bukatar gani an mutunta 'yancin dan'adam.
Daga karshe shahararriyar mawakiya Hajiya Hamsou Garba, ta mika kiranta ga shugaban kasar Nijar Mahammadu Isuhu inda ta ce ya dawo kujerar sulhu tare da dan uwansa amininsa Hama Amadou domin ci gaban kasar Nijar.
Ga rahoton da Abdoulaziz Adili Toro ya hada muna daga birnin New York.
Facebook Forum