Kasar Iran ta gargadi kasashen tarayyar turai kan mayar da martani ga kokarin da take yi na haura adadin sinadarin Uranium da aka kayyade mata karkashin yarjejeniyar nukiliya da aka kulla a 2015.
Najeriya, wacce ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, ta shiga yarjejeniyar kasuwancin nahiyar tare da Jamhuriyar Benin. Yanzu haka, Eritrea ce kadai ba ta shiga yarjejeniyar ba wacce masana suka ce za ta iya samar da hanyoyin kasuwanci da kudinsu zai kai dala biliyan 3.4.
A Sudan, sojojin dake jan ragamar mulkin kasar sun cinma wata matsaya da masu fafutukar maida kasar bisa tafarkin demokaradiyya, inda za'a dinga mulkin kama-kama, kana da samar da kwamnati mai zaman kanta, wanda Firai Minista zai jagoranta
Shugaban kasar Rsaha Vladimir Putin ya ce lalai ne wani jirgin ruwan soja dake karkashin teku dake dauke nukiliya ya kama da wuta, ya yi sanadiyar mutuwar mai’aikatan jirgin su 14, amma yace jirgin bai yi muguwar lalacewa.
A wani taro manema labarai da ya kira a Yamai shugaban Hukumar dake kula da shirye-shiryen wannan taro Saidine Moctar Mohamed ya bayyana alfanun wannan taro ga nahiyar Afrika da kuma irin matakan tsaron da kasar Nijar ta dauka.
Rahoton hukumar kula da ‘yan gudun hijira a Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara, ya gano cewa kusan mutane miliyan 13.6 suka rasa matsugunnansu a cikin shekara daya sanadiyar yaki ko kuntatawa.
Afganistan: Wani bom mai karfin gaske da hare-haren bindiga a Kabul sun kashe mutane da yawa, yayin da wasu da dama suka ji raunuka.
Sudan: A Sudan, dubun dubatar masu zanga-zanga sun taru suna kira da a mika mulki ga farar hula, bayan kusan watanni uku da sojoji suka hambarar da Omar al-Bashir wanda ya yi shekara da shekaru yana mulki.
A Japan mutane fiye da 100 ne suka yi zanga zanga a Osaka domin nuna kin amincewa da rahoto da kungiyar kare hakin bil adama ta China ta fitar mai alaka da muslmin kasar na kabilar Ugighurs a Hong kong yayinda ake gudanarda da taron G20.
A Tunisiya jami’ai ke ci gaba da yin bincike domin neman sanin ko wanene ke bayan hare-haren kunar bakin wake guda biyu da suka kashe dan sanda daya da raunata wasu mutane 8 da suka hada da yan sanda.
Biyo bayan hare-haren bomaboman da aka kai a sassan jihar Borno, matasan yankin sun bayyana ra’ayoyinsu akan hanyar da suke gani za a iya magance wannan matsala.
Iran ta kakkabo wani jirgin saman Amurka mara matuki a wani lamari da jami’an kasar su ka ce ya faru a sararin samaniyar yankin Iran amma jami’an Amurka sun ce a wani sararin samaniyar kasa-da-kasa lamarin ya auku.
A Libya, mayakan dake goyon bayan gwamnatin hadin kan kasar da kasashen duniya suka fi amincewa da ita sun yi arangama da dakarun khalifa Haftar a yankin Alsawani dake kudancin birnin Tripoli.
A Habasha jami’ai daga kasashe daban daban suka hadu a Addis Ababa domin tattaunawa kan rikicin Sudan, wanda ya fuskanci mummunan farmaki da aka kai akan masu zanga zanga, lamarin da ya kai mutuwar wasunsu
Anan Amurka a jiya talata ne jami’an tsaron na tarraya suka ba da sanarwar kama ton 16 na hodar iblis a gabar tashar jiragen ruwa a jihar Philadelhia.
Domin Kari