Rabecca Sharibu, mahaifiyar dalibar nan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace a makarantar kwanan ‘yammamata dake Dapchi, da ta kasance daya tilo da har yanzu ba a sako ba, ta ziyarci ofishin Muryar Amurka.
Sugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya sanar a yau Laraba cewa, rana Jumma’ar nan me zuwa ne dakarun hadin guiwar kasashen Turkiyya da na Russia zasu fara wani sintirin hadin-gwiwa a Syria, rana daya bayan wa’adin da aka gindayawa mayakan Kurdawan Syria su janye dakarunsu daga yankin.
A Kenya, gungun wani iyali sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya kaddamar da bincike akan yadda Turawan Mulkin Mallakan Birtaniya suka kore su daga gidansu dake yammancin Kasar shekaru tamanin da suka gabata. Lauyoyin Ingila da Kenya ne ke wakiltar iyalin
A wata ziyara aiki da tsohon shugaban Kasar Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya kawo nan Washington, Muryar Amurka ta samu tattaunawa da shi akan al’amuran da suka shafi Najeriya da ma nahiyar Afrika gaba daya
Abdoulaye Madassane Alkika na daya daga cikin masu kidar garaya dake tare da wasu matan abzinawa mawaka su uku da suka fara kawo ziyara a nan Amurka daga Jamhuriyar Nijar. Mata mawakan sun zagaye jihohin Amurka inda suka rera wakokin gargajiya domin nishadatar da masu kallo.
Firayim Minista Justin Trudeau ya yi ikirarin samun nasara a jiya Talata bayan da ya sake lashe zabe a karo na biyu a babban zaben kasar.
Rasha: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya isa Sochi don halartar dandalin tattaunawar tsakanin Rasha da Afirka. Kremlin ta ce ana zaton shugabannin kasashen Afirka 47 ne za su hallarci taron da za’a gudanar daga ranakun 23-24 na Oktoba, wanda shine babban taron Moscow da Afirka na farko.
A jiya Litinin ne wanda ya kirkiro shafin WikiLeaks Julian Assange ya gurfana gaban wata kotun a London, don yaki da tasa keyarsa zuwa Amurka bisa zargin leken asiri.
'Yan sanda sun ceto dalibai kusan 150, daga wata makaranta a arewacin Nijeriya, da suka ce tana koyar da karatun Kur'ani, amma, a maimakon haka, take gallaza masu azaba.
A wata hira ta musamman da yayi da Muryar Amurka, Shugaban rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce duk wanda zai yi la’akkari daga "inda aka faro da kuma inda ake a yanzu lallai zai san gwamnatin Najeriya tana kokari sosai."
Domin Kari