An shiga kwanaki biyu da zanga-zanga a fadin kasar Lebanon a yayin da mutane suka yi tattaki a Beirut jiya Alhamis da yamma suna nuna rashin jin dadinsu akan kamun ludayin gwamnatin kasar game da matsalolin tattalin arziki.
Wata kotu a Guinea ta yi watsi da karar wasu shugabannin jam’iyyun adawa su 8 da aka zarga da shirya zanga zangar kin jinin yinkuri shugaba Alpha Conde na sake neman wa’adin shugabanci karo na 3, bayan da wani sabon rikici ya barke a birnin Conakry.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tofa albarkacin bakinta dangane da gidajen azabtar da yara da sunan gyara tarbiyya a jihar.
'Yan sanda a arewacin Najeriya sun kubutar da wasu samari sama da 300 daga wata makarantar kwana ta islama, inda aka ba da rahoton cewa an daure su da kuma lalata da su. An ceto su ne ranar Talata a yankin Daura, bayan da wasu daliban suka tsere suka sanar da ‘yan sanda.
Jami'an Turkiyya sun ce Shugaba Rejep Tayyip Erdowan, zai gana da Mataimakin Shugaban Kasar Mike Pence da Sakataren Harkokin Wajen Mike Pompeo bayan sun isa Turkiyya don matsa lamba kan dakatar da mamayar da Turkiyya ke yi a arewa maso gabashin Siriya.
Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukan su bayan da mahaukaciyar guguwa Hagibis ta abka a Japan ranar Asabar
Fitacciyar mawakiyar nan 'yar Najeriya kuma ‘yar Birtaniya Theresa Lola tana gudanar da wani taron bita a Abuja. A matsayinta na mai rikon lambar yabon YounG People’s Laureate na Landan, tana kokarin baiwa 'yan matan da suka fito daga yankin da’ake rikici dama.
A Jamhuriyar Nijar kuma kasar Amurka ta tura wata tawaga da ta kunshi wasu mata futattu a majalisar kasar da suka hada da Karen Bass, da Ilhan Omar domin ganawa da gwamantin shugaba Muhammadu Issfufu
a Tunisia, an saki Dan Takara shugaban kasa Nabil Karoui daga gidan yari, ‘yan kwanaki kafin zaben fidda gwanin da za a yi a kasar
Kamfanin Apple, ya cire wata manhajar wayoyin zamani dake baiwa masu gwagwarmayar Hong Kong damar bada rahoton zurga-zurgar jami’an ‘yan sanda daga rubun manhajarsa ta yanar gizo bayan da wata jarida mallakar gwamnatin China ta zargi Apple da taka rawa wajen aikata munanan dabi’u.
A jamhuriyar Nijar Ma’aikatar kula da mata da yara, tare da gudunmawar wasu kungiyoyin mata sun kai kayan agaji ga mutanen da ko wacce shekara ke fama da matsalar ammbaliyar ruwa.
Binciken ra’ayin jama’a ta nuna wata jam’iyya mai kishin Islama a matsayin wacce ke samun karbuwa a majalisan dokokin Tunisiya makonni biyu bayan zaben shugaban kasa da ya sauya yanayin siyasar kasar.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce Sojojin Amurkan sun fara janyewa daga inda suka ja daga a arewacin Siriya, sa'o'i bayan Fadar White House ta sanar da cewa sojojin ta za su bar yankin don share fagen shiga Turkiyya.
Wata kungiya mai suna D.O.B mai yaki da gurgusowar hamada da canjin yanayi ta hanyar koyawa mazamna karkara sassabe na zamani domin a bar kashe itace , ta dauki aniyar raya wani hili da ke dauke da ma'aikatar magajin garin Allela a cikin gundumar Birni N'Konni.
Domin Kari