Tuni har an riga an yi masa karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai, kuma idan wanan kuduri ya samu shiga, Majalisa za ta iya tilasta Shugaban Kasa da Gwamnoni su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyin da aka bijiro masu a duk lokacinda bukatar hakan ta taso.
Wadansu 'yan bindiga da a ke kyautata zaton masu tsattsauran ra'ayin addini ne da suka kutso daga kasar Mali, sun abka wa garuruwa 2 na gundumar Tilliya a cikin jahar Tahoua jamhuriyar Nijar, su ka kashe mutane 54.
A Tanzania ne Samia Suluhu Hassan mai shekaru 61 da haihuwa ta kafa tarihi bayanda aka rantsarda ita a matsayin shugabar kasar mace ta farko a Dar Es Salam. Ta zama shugabar kasar ce bayan mutuwar John Maguful ranar laraba da ta gabata
A Kongo dakarun soja suka fara kada kuri'unsu a zaben shugaba kasa gabanin ranar zaben 21 ga watan Maris. Shugaba Denis Sassou Nguesso zai kara da yan takara 6 amma yana ganin cewa zai kara lashe zaben.
An dade ana muhawara kan kayyade iyali. Wadanda su ke bayan matakin suna masu ra’ayin cewa, yana taimakawa wajen samun ingancin rayuwar mata da yara da kuma bunkasa tattalin arziki. Wadanda kuma su ke gaba da tsarin kuma galibi suna yi ne bisa dalilai na addini ko al’ada.
Wani rahoton bankin duniya na 2020 da 2021 ya ayyana Jamhuriyar Nijer a matsayin daya daga cikin kasashen da suka sami ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afurka sai dai ‘yan kasar na nuna ra’ayoyi mabambanta a game da wannan rahoto
Ranar takwas rana ce ta tunawa da gudunmowar da mata ke badawa, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe don duba matsaloli, koke koke da bukatun mata na duniya
Domin Kari