Zuckerberg Da Matarsa Priscilla Sun Samu Karuwa

Mark Zuckerberg Jarvis

Ma’auratan na da wasu ‘ya’ya mata biyu, August mai shekaru biyar da Maxima mai shekaru bakwai.

Shugaban kamfanin Facebook da ke karkashin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya samu karuwa da ‘ya mace.

Zuckerberg da mai dakinsa Dr. Priscilla Chan ne suka sanar da haihuwar ‘yar ta su mai suna Aurelia a ranar Juma’a.

Haihuwar Aurelia na nufin ‘ya’yansu sun zama uku kenan.

Ma’auratan na da wasu ‘ya’ya mata biyu, August mai shekaru biyar da Maxima mai shekaru bakwai.

Tun a watan Satumba suka sanar cewa za su samu karuwa inda suka ce Maxima da August za su samu kanwa.

Mark da Chan sun hadu ne a shekarar 2003 a jami’ar Havard, sun kuma yi aure a shekarar 2012.