Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake kai ziyarar aiki jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin kasar, don kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta kammala.
A ziyarar da ya fara a yau Alhamis, Shugaba Buhari zai shafe kwana biyu yana kaddamar da wasu jerin ayyuka, kamar su kasuwar kasa da kasa ta Margaret Umahi, da sabon gidan gwamnati, da sabon ofishin gwamna, da jami'ar kimiyar lafiya ta King David, da hanyar Uburu-Mpu wacce aka fadada, da dai sauran su.
Kakakin kungiyar Dakta Alex Ogbonnia ya ce, "muna amfani da wannan damar ne mu roke shi ya tuna abubuwa biyun da muke bukatarsa ya yi. Daya shi ne lokacin yankin kudu maso gabas ne ya kawo wa Najeriya shugaban kasa. Biyu shi ne har yanzu Ohanaeze na rokon afuwa ga Nnamdi Kanu, tare da neman sulhu don warware batun Nnamdi Kanu da sauran batutuwan da ke shafar matasan kasar Igbo."
Mista Chisom Igboko wani mai fashin baki ne kan lamuran siyasa, ya kuma ce ziyarar Buhari a jihar ta Ebonyi abin tarihi ne.
"Ziyarar shugaban kasa jihar Ebonyi kyakkyawar nasara ce sosai ga gwamnan jihar Dave Umahi. Kuma dole ne mu yaba wa gwamnan bisa ayyukan ci gaban da ya aiwatar. Wannan ziyarar na nuna kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin gwamnan da gwamnatin tarayya. Kuma ziyarar za ta kara buda wasu daman ga al'ummar jihar."
"Ziyarar za ta yi tasiri kadai idan shugaban kasan yana da wata sanarwar da zai yi da za ta amfani yankin kudu maso gabas a fannin bunkasa ayyuka, ko kuma a wani fannin. Banda wannan, cewa ya zo ne don ya kaddamar da wasu ayyuka kawai ba zai yi wani tasiri ba." Dakta Celestine Nwosu, wani malamin jami'a ya ce kan tasirin ziyarar Buhari.
Wannan shi ne karo na uku da Shugaba Buhari ke kai ziyara jihar ta Ebonyi, na farko a watan Nuwamban shekarar 2017, na biyu kuma a watan Janairun shekarar 2019.
Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okorigwe:
Your browser doesn’t support HTML5