Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Zuwa Saudiyya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry.

Rikicin kasar Siriya na daya daga abin da ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry zuwa Saudiyya da Faransa za ta maida hankali akai. Tattaunawar da Kerry zai yi da jiga-jigan Saudi a ranar Juma’a da Asabar zai biyo bayan shirye-shiryen Majalisar Dinkin Duniya ne na ci gaba da tattaunawar bangarorin Syria game da makomar siyasar kasar.

Duk da yake dai bangarorin ‘yan adawa na ta alamta kila-wa-kalan ko zasu halarci zaman a birnin Geneva ko a’a. bangaren ‘yan adawar na zargin gwamantin Syria ne game saba yarjejeniyar tsagaita wuta da kai hare-hare a karshen watan Fabrairun da ya gabata.

Amurka da Saudiyya dai na cikin kasashe 17 da ke tallafawa Syria, tare da goyon bayan dawo da zaman lafiya a siyasance ga al’ummar kasar. Ma’aikatar wajen Amurkar ta ce kasar Yamal ma na daya daga inda ziyarar ta Kerry zata waiwaya.

Inda sojojin taron dangin da Saudi ke jagoranta ke ta faman cilla bama-bamai ta sama zuwa kan ‘yan tawayen shi’ar Houthis. Sakataren zai zarce zuwa birnin Paris kai tsaye bayan ya tashi daga birnin Hafar al Batin ta kasar Saudiyya.