Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Nazarin Wasu Bayanai Da Aka Samu Kan Kungiyar ISIS


Kwararrun masana harkar magance ayyukan ta’addanci a Jamus hade da na sauran kasashen duniya na ta nazarin wasu dubban bayanan da ake zaton daga yanar gizon kungiyar ISIS da aka sato su. Bayanan da ke nuna akwai yiwuwar samun cikakkun bayanan yadda suke daukar mayakan sa kai.

Wani gidan Talbijin SKY NEWS a Birtaniya yace, an sami wannan kundin bayanan Kwamfutar ne daga wani dan membar ISIS da Kungiyar ta fusata shi, kamar yadda ya fadawa wani dan jarida a Turkiyya. Yace ya sace wata ‘yar naurar ajiye bayanan ne daga shugaban tsaron cikin gidan kungiyar.

Sannan wannan ‘yar naurar Kwamfiyutar tana nade da bayanan membobin ISIS akalla guda Dubu 22, wanda suka hada da mayaka da magoya bayan kungiyar. Jami’an ‘yan Sandan Jamus sun fadawa kamfanin dillancin labaran AP cewa akwai kanshin sahihancin wannan matattarin bayanan da aka samu.

Rahotanni daga Birtaniya, Jamus da Syria sun ce, wannan kundin bayanan Kwamfutar ya kunshi akalla bayanan masu ikirarin Jihadi daga kasashen duniya 51. Ciki bayanan akwai wasu tambayoyi gudfa 23 da ake wa masu son zama membobin ISIS da sai ka amsa kafin a daukeka a kungiyar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG