Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari na ziyarar a birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya je domin halartar taron sojin kasar da ake yi a kowacce shekara.
Ziyarar ta Buhari na zuwa ne, a daidai lokacin da ake ci gaba da jimamin kisan wasu sojin kasar da ake zargin kungiyar Boko Haram da aikatawa a yankin Metele.
Rahotanni da dama sun ce sama da sojoji 100 aka kashe a wannan hari, ko da yake, rundunar sojin kasar ba ta fito ta fadi takamaiman adadin sojojin da ta rasa ba, duk da cewa ta tabbatar da aukuwar harin.
Wakilinmu Haruna Dauda Biu da ke Maiduguri ya ce Buhari ya fara ziyarar ce da kai gaisuwa a fadar Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garba.
Sannan ya kai ziyarar asibiti domin yin jaje ga sojojin da suka samu raunuka a harin na Metele.
Saurari hirar da Mahmud Lalo ya yi da Haruna Dauda Biu kan ziyarar ta Muhammadu Buhari:
Your browser doesn’t support HTML5