Shugaban kungiyar kuma gwamnnan jihar Zamfara Abdul’ziz Yari, wanda ya jagoranci takwarorinsa daga fadin Najeriya don jajantawa al’ummar Filato, bisa hare-haren da suka hallaka jama’a masu yawa, ya ja hankalin ‘yan ‘kasa baki daya cewa babu wani ci gaba da za a samu idan har ba a zauna lafiya ba.
A cewar gwamna Abdul’aziz Yari, kungiyar gwamnonin ta yanke hukuncin kai ziyarar jaje ga gwamna da al’ummar Filato baki daya, tare da neman hanyoyin da za a iya bi wajen samar da zaman lafiya.
Shi ma gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura, wanda ya jagoranci daukacin sarakunan gargajiyan jihar da sauran kusosin gwamnatinsa don yin jajen, ya ce duk wani abin da ya sami jihar Filato tamkar ya shafi jihar Nasarawa ne.
Da yake godewa bakin na sa gwamnan jihar Filato ya Simon Lalong, ya ce ziyarar da shugaban ‘kasa da mataimakinsa da duk sauran jiga-jigan masu mulkin ‘kasa suka kawo jihar Filato, ya nuna irin ‘kaunar da ake yi wa jihar.
Shima shugaban jam’iyyar APC ta ‘kasa Adams Oshiomhole, ya tafi Jos don nuna alhininsa kan kashe-kashen da ya faru a jihar.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5