Bayanin da gwamnatin Najeriya ta fitar ya nuna cewar likitocin shugaban kasar ne suka bashi shawarar cewar idan yaje Ingila yaje kwararrun likitoci su kara dubashi dan gane da matsalar da yake fama da ita.
Sai dai kuma ‘daya daga cikin likitocin Najeriya kuma mai fashin baki Dakta Abu Yazid, yace a ganin ba yadda za ayi ace babu kwararrun likitocin da ba zasu iya duba shugaban ba a Najeriya, sai dai in har ba a bincika ba.
Duk da yake idan mutum ya bar Najeriya domin zuwa a duba lafiyarsa ya kan tarar da kwararrun likitoci ‘yan Najeriya na aiki a kasashen waje. Babbar matsala itace rashin kayayyakin aiki da likitoci ke bukata a Najeriya.
Tun farko kafin tafiyar shugaba Buhari, ya shaidawa manema labarai cewa ba abin mamaki bane cewa yayi rashin lafiya, saboda kowanne mutum na iya samun ciwo. Wannan magana da alamu yana mayar da martani ne ga masu cecekuce dangane da wannan larurar da yake fama da ita.
Your browser doesn’t support HTML5