Hakan na zuwa ne yayin da yan Najeriya ke kokawa game da matsalar rashin kudi. Mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya mai kula da jihohin Arewa 19 Alhaji Mohammed Ibrahim, yace kullun burunsu shine a samu sauki a rayuwa musamman ma a wannan lokaci na samun lada.
Watan nan dai lokaci ne da al’ummar musulmi ke kara kaimi a ayyukan ibada, inda ma ake wadatar da iyali da abinci, shine koya al’umma suka fara Azumi a wannan shekarar?
A bana ma dai watan Azumi ya kawo fahimtar juna a tsakanin al’umomin da rikicin Boko Haram ya shafa, musamman ma a Arewacin jihar Adamawa wanda a baya ya fada hannun Boko Haram, Mista Adamu Kamale Dan Majalisar dake wakiltar Madagali da Michika a Majalisar wakilai, yayi kira da a hada kai don yin addu’o’in neman zama lafiya a wannan watan mai albarka.