WASHINGTON, DC —
Al’ammura sun dawo dai-dai a birnin Khartoum inda aka sake bude shaguna a kasuwanni kuma zirga-zirgar abubuwan hawa ta dawo kan tituna, bayanda kungiyoyin adawa suka kammala tarukkansu na zanga-zanga da yajin kin zuwa wurarensu na aiki.
Nan bada jimawa ba ake sa ran wakilan masu zanga-zangar zasu sake komawa kan teburin tattaunawa da shugabannin gwabnatin mulkin soja ta kasar akan hanyoyin maslaha.
Sojojin dai da ke rike da mulkin kasar tun bayanda suka tumbuke tsohon shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilu, sun yarda zasu saki fursunonin siyasa, a cewar jagoran sulhu na musamman daga kasar Habasha Mahmoud Dirir.