Zazzabin Cizon Sauro Ya Yi Tsanani Bana a Jamhuriyar Nijer

Yayin da alkaluma ke nuna cewa cutar maleriya ta yi tsanani a Jamhuriyar Nijar a wannan shekarar, alamu na nuna cewa mutane wajen 2000 ne cutar ta hallaka a kasar bana.

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Nijer sun tabbatar da rasuwar mutane sama da 2000 a bana sakamakon kamuwa da zazzabin cizon Sauro wato Maleriya, lamarin da ake dangantawa da ruwan saman da aka tafka, wanda kuma ya haddasa ambaliya da karuwar tafakuna.

Miliyoyin mutane sun kamu da zazzabin cizon Sauro daga farkon shekara zuwa farkon watan Oktoban shekarar nan, abinda ya yi sanadiyar rasuwar mutane sama da 2000 lamarin da minstan kiwon lafiyar al’umma Dr. Iliassou Idi Mainassara ya dangantashi da sakacin jama’a game da daukar matakan riga kafi.

Domin tunkarar wannan matsala gwamnati ta yi tanadin miliyoyin magunguna da ta umurci likitoci su bai wa marassa lafiya kyauta inji ministan.

A cikin matakan magance cunkoson marassa lafiya da ake fuskanta a manyan asibitoci a wannan lokaci, masu fama da zazzabin cizon Sauro, hukumomin kiwon lafiyar kasar sun gargadi jama’a da su fara zuwa asibtocin unguwanni, domin samun shawarwari daga likitoci.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Bita Kan Cutar Maleriya a Nijar