Ministar karfafa gwiwa ga matan Kamaru, Marie Therese Abena Ondoua, ta ce har yanzu ana aiwatar da al'adun gargajiya da ke take hakkokin zaurawa a sassan kasar.
Njoukou Yebom mai shekaru hamsin da takwas ya fito ne daga Noun, wani sashin da ke yammacin Kamaru. Yebom ya ce ya yi nadamar cewa ya yi yunkurin tilasta wa matar kaninsa marigayiya mai shekara 15 ta aure shi.
Yebom ya ce a cikin shekarar 2018, dattawa a garin Foumban inda Noun ta ke sun nemi ya auri matar marigayin dan uwan nasa mai shekaru 30. An ce masa idan ya ƙi auren matar, wani baƙo na daban zai gaji dukiyar ƙaninsa kuma ya tafi tare da ɗansa tilo. Yebom ya ce ya yi barazanar kashe ta idan ta ki.
Surukar Yebom ce ta kai kararsa ga Ma’aikatar bada Tallafin Mata. Ya ce ‘yan sanda sun cafke shi kuma sun tsare shi saboda yunkurin sace dukiyoyi da kuma yin barazana ga rayuwar yarinyar.
Sauran al'adun sun hada da tilasta wa mata su kwana da gawarwakin mazajensu da suka mutu da shan ruwan da aka yi amfani da su wajen yin wanka a jikinsu a matsayin wata alama da ke nuna cewa ba su kashe mazajensu ba.
Amy Banda, shugabar kungiyar Target Peace, wata kungiya mai zaman kanta da ke kare hakkin zaurawa, ta ce kungiyarta na son su hana mata su daina tilasta ka’idojin zaurawa ga takwarorinsu da suka rasa mazajensu.
Francisca Moto, jami'i mai kula da ingantawa da kare iyali a ma'aikatar karfafa gwiwar mata, ta ce har yanzu ana ci gaba da cutar da zaurawa a Kamaru saboda jahilci da tasirin maza.
Moto ta ce "Wadannan munanan dabi'un akan alakantasu ne da maita don haka mutane na tsoron rabuwa da al’adun, don mai yuwuwa su rasa 'ya'yansu, shi ya sa dole ne a ci gaba da daukar matakai."