Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano:Tasirin Auren Zaurawa na Gamayya


Wasu daga cikin zaurawan da aka aurar a shekarar 2012
Wasu daga cikin zaurawan da aka aurar a shekarar 2012

A watan Mayun shekarar 2012, gwamnatin Jihar Kano ta fito da wani tsarin aurar da daruruwan zaurawa a wani mataki na ganin an dakile matsalar yawan mace-macen aure a jihar.

Kafin aiwatar da auren, an bi ka’idoji na gwaje-gwajen cututtuka musamman cutar nan mai karya garwakuwar jiki ta kanjamau ko kuma SIDA, baya ga kayan daki da sadaki da ake baiwa amare.

Tun bayar da kaddamar da wannan tsari, an yi shi a kashi daban-daban kusan kashi biyar.

Masu saka ido akan al’amuran yau da kullum na tambayar ko wannan aure na tasiri? Wakiliyar Sashen Muryar Amurka a jihar Kano, ta bi diddgin wasu da suka amfana da wannan aure da hukumar dake kula da lamarin.

“Ina da mata na guda biyu, sai na kara ta uku, kuma yanzu haka har ma mun aihu.” In ji Lawal Ali Dala, daya daga cikin wadanda suka amfana da wannan aure.

Ita kuwa Malama Nafisa Sharif Salisu cewa ta yi “aure dai dama wajibi ne akan ‘ya mace, sannan kuma ga wannan tagomashi da gwamnati ta yi. Duk abinda ya iyaye ya kamata su yiwa ‘ya sun yi.”

Yanzu haka bincike na nuna cewa an samu haihuwar jarirai 260 ciki har da ‘yan tagwaye daga auren na zaurawa tun bayan da aka kaddamar da shi a shekarar 2012.

“Tsare wannan matsalar mutuwar auren ne ya sa muka yi wani kwamiti da zai dinga bin diddigi, muka zuba mata a ciki, tun da kowane muna da adreshinsa da gidansa, su suke bi gida gida suke gaya mana idan akwai wata matsala, sai mu kira su mu shiga tsakani.” In ji Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda shi ne shugaban Hisba a Jihar kano.

Ya kuma kara da cewa daga cikin aure 4,922, guda goma ne kawai suka sami matsala ya kuma kara da cewa akwai matakan da suke dauka ga duk wanda ya ke so ya saki mata ba tare da wani dalili ba.

“Duk mutumin da ya yi aure a hannun mu zai saki matar kuma ba dalili, zai biya matar dubu 250 zuwa dubu 50, mun sami mutum guda ya bukaci ya saki matarsa daga yankin Madobi kuma ya biya wannan kudin bayan da aka sayar da gonarsa.” In ji Sheikh Daurawa.

Ga karin bayani a wannan rahoton na Baraka Bashir:

Shin Auren Zaurawa Na Gamayya Na Tasiri? - 3’03”
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG