Dubban al'uma daga sassa daban-daban na Najeriya ne su ka halarchi sallar Jana'izar marigayi mai-martaba Sarkin Zazzau abin da yasa sama da rabin mutanen da ke gurin har aka ida sallar ma ba su sani ba.
Wakilan shugaban Kasa, da gwamnan jahar Kaduna da mukarraban shi da kuma manyan sarakunan arewa na cikin wadanda su ka halarci sallar Jana'izar.
Haka ma mai-martaba sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayaro na cikin masu zaman makoki. Ya kuma ce "wannan rashi ya yi girman da baya misiltuwa kana rashi ne da ya shafi masarautar Zazzau da jihar Kaduna da al’ummar Arewa da ma Najeriya baki daya."
Dallatun Zazzau kuma tsohon gwamnan jahar Kaduna Muktar Ramalan Yero da kuma Dan-buran Zazzau Alhaji Sani Mahmud Sha'aban, 'yan cikin gida ne a masarautar Zazzau. Sun bayyana alhinin su inda suka ce sun yi rashin shugaba kuma uba, "saboda haka wannan babban al’amari ne a kan masarautar Zazzau."
Mata dake cikin gidan sarautar Zazzau ma suna cikin juyayi na wannan babban rashi da aka yi.
An haifi marigayi mai-martaba sarkin Zazzau Alh. Shehu Idris ne a watan Maris na a shekarar 1936 inda aka nada shi sarki a shekarar 1975 lokacin ya na da shekaru 39 kuma a watan Fabarairun wannan shekara ne ya cika shekaru 45 a kan karagar sarautar Zazzau.
Kafin rasuwar sa a jiya Lahadi ya yi zamani da gwamnoni daban-daban har goma sha tara a jihar sa ta Kaduna.
Ga dai raohon Isah Lawal Ikara daga Kaduna, a Najeriya:
Your browser doesn’t support HTML5