Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya maka Majalisar Dokokin jihar a kotu akan ikirarinta na zargin cewar gwamnatinsa ta shekaru 8 ta wawure naira biliyan 432 inda ta bar jihar cikin dimbin bashi.
A yau laraba ne El-Rufa'i ya maka Majalisar Dokokin Kadunan a gaban babbar kotun tarayya dake jihar akan tauye masa hakkokinsa.
Karar wacce lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem Mustapha, mai lambar Babban Lauyan Najeriya (SAN) ya shigar ta kalubalanci rahoton kwamitin majalisar wanda ya samu El-Rufa'i da laifin aikata almundahana.
A kunshin karar, El-Rufa'i ya bukaci kotun ta ayyana rahoton binciken majalisar a matsayin mara tushe kasancewar bai bashi damar kare kansa daga zarge-zargen da kwamitin ke yi masa tare da gwamnatinsa ba.
Wadanda ke cikin kunshin karar sun hada da Majalisar Dokokin Kadunan da antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar.