Reshen jihar Kano na kungiyar kwadagon Najeriya ya bi sahun takwararorinsa na jihohin kasar wajen gudanar da zanga zangar lumana zuwa majalisar dokoki domin nuna kyamarsu ga yunkurin majalisar tarayya kan mallaka hurumin kayyade albashi daga hannun gwamnatin tarayya zuwa gwamnatocin jihohi.
Kwamrad Kabiru Ado Minjibir, shugaban kungiyar kwadagon Najeriya a jihar Kano, lokacin da ya jagoranci gamayyar kungiyoyin kwadogo karkashin NLC zuwa harabar majalisar dokokin Kano, ya jaddada wannan matsayin.
Wakilin mazabar sabon garin Zaria a zauren majalisar wakilan Najeriya, honarabul Garba Datti Mohammed shi ne ya gabatar da wannan kuduri a zauren majalisar wadda har ya tsallake karatu na biyu, kamar yadda shugaban kwadagon na Kano ya yi Karin bayani da cewa, "Fargabar ita ce idan wannan kudurin ya tsallake, za a kai lokacin da wasu gwamnoni za su dinga yadda su ka ga dama da albashin ma'aikata, ko dai su biya ko su yi yadda suke so."
Duk da cewar akwai tsarin biyan albashi mafi karanci da ake da shi a kasar, ba a mutunta shi ba, ina ga idan wannan dokar ta kankama?
Bayan karbar wasikar ‘yan kwadagon, shugaban majalisar dokokin ta Kano Hon Hamisu Ibrahim Chidari ya ce, "Muna baku tabbacin koken ku za a duba shi da idon da ya dace da shi, muna kuma yaba muku kamar yadda kuka zo cikin natsuwa, da maslaha, kuka shigar da kokenku, zamu duba shi kamar yadda doka ta tanadar."
Hon Lawan Hussaini da ke zaman shugaban kwamitin majalisar dokoki kan sha’anin ma’aikata da ayyukan gwamnati ya fayyace hanyoyin da dokokin su ka yi tanadi gabanin wannan kudirin ya kai ga nasara.
Ya ce, "Za mu duba koken ta yadda ya dace, duk kuwa da cewar sai an bi abun da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar wajen gyara da cusa wani abu a cikin kundin."
Za a iya sauraron rahoton Mahmud Kwari a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5