Zanga Zangar Juyin Juya Hali Ya Shiga Wani Hali

‘Yan sanda Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta girke jami’anta a muhimman sassa kamar mahadar tituna don rigakafin gudanar da zanga-zangar juyin juya hali daga wasu kungiyoyin da’awar tsaro da dimokradiyya.

Wadannan matakan ne suka yi sanadiyar cunkuson ababen hawa a wasu titunan gefen Abuja da ba a faye samun hakan ba da rana tsaka.

Akalla dai wata kungiyar tattaunawar musulmi da kirista da jagorancin Pasto Simon AS Dolly ta gudanar da taro don nuna rashin amincewa da zanga-zangar.

Taron a masaukin baki na majami’ar Katolika dake unguwar Zone 6 a Abuja ya bukaci masu zanga-zangar su janye matsayar su da bin matakin tattaunawa don warware abin dake damun su.

Tijjani Abdulmumin dake jagorantar bangaren matasa a kungiyar, yace duk da akwai matsalar kuncin rayuwa a mulkin da ke kan gado, amma in a ka yi la’akari da yadda fitina kan durkusar da kasa, barin fito-na-fiton ya fi alheri.

An samu labarin a Lagos an so gudanar da zanga-zangar inda ‘yan sanda su ka jefa hayaki mai sa kwalla da kuma kama wasu mutane.

Madugun zanga-zangar juyin juya hali Omoyele Sowore na hannun ‘yan sandan farin kaya DSS.

Magoya bayan Sowore sun garzaya hukumar kare hakkin ‘yan adam inda su ka nemi a sake shi da nuna su na da ‘yancin bayyana ra’ayin su.

Haka nan sun yi zargin an so murkushe da dai sun yi yunkurin isa dandalin bayyana ra’ayi na UNITY, inda ‘yan sanda su ka taru a bigiren don dakile masu son zanga-zangar ta kin jinin gwamnati.Hakanan da sojojin haya da su ka zo a motocin safa biyu don birkita muradin.

Ga rahoton wakilin Nasiru Adamu Elhikaya daga birnin Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

MASU ZANGA ZANGAA JUYIN JUYA HALI