Wata babbar kotu a Kaduna, ta ba shugaban Islamic Movement of Nigeria (IMN) ta ‘yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El Zakzaky, damar zuwa India neman magani, amma tare da rakiyar jami’an tsaron farin kaya na DSS.
Kotun har ila yau, ta ba uwargidan El Zakzaky, Zeenat izinin zuwa neman maganin ita ma.
Alkalin kotun, mai shari’a Darius Khobo ne ya yanke hukuncin a yau Litinin, bayan da ya dage zaman sauraren karar zuwa yau.
Lauyoyin El Zakzaky, sun nemi kotun ta ba shugaban mabiya Shi’ar damar ya je kasar waje neman magani da shi da mai dakinsa Zeenat, saboda rashin lafiya da suke fama da ita.
Tun a shekarar 2015 hukumomi suke tsare da shi da iyalinsa, bayan wani dauki-ba-dadi da aka yi tsakanin mabiyansa da dakarun Najeriya.
Hukumomin Najeriya na tuhumar shi da laifin kisa da ta da tarzoma, yayin da mabiyansa suke zargin an kashe masu daruruwan mambobi tare da rusa gidan shugaban nasu.
A baya, wata kotu ta taba ba da iznin a sake shi a kuma biya shi diyya, amma mahukuntan Najeriya sun kalubalanci matsayar kotun, lamarin da ya sa har yanzu yake tsare.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna: