Zanga-zangar neman kawo karshen sashen rundunar 'yan sandan SARS da ake zargi da cin zarafin al’umma fiye da kima a Najeriya ta tafi ta bar baya da kura inda aka samu rarrabuwar kawuna ta fannin kabilanci da addini a cewar shugaban al’umma Pigba Mr. james, wanda ke yankin da aka kona shaguna da motocin al’umma a lokacin da rikicin ya barke a Abuja.
A duk lokacin da aka samu rikici irin wannan a Najeriya ana yawan nuna wa malaman addini yatsa a game da yadda rikici ke ta’azzara ta irin hudubobin da su ke yi wa mabiyansu inda lokuta da yawa suke kaucewa daga koyarwar addini.
Sheik Dahiru Bauchi, Babban malamin addinin Islama ne, ya yi kira ga malaman addini da su tsaya akan abinda ke daidai ya kuma jaddada muhimmancin jin tsoron Allah da yin adalci musamman ga malaman addini, da shugabannin al'umma, da kuma mahukuntan kasa.
Sheik ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya akan ta sauke hakkin da ke kanta ta kuma duba abubuwan da ke faruwa a kasar, kama daga batun matsin rayuwa, tsaro, rashin aiki da sauransu.
A na sa bangaren, shugaban gudanarwa na gidauniyar zaman lafiya ta Duniya a Najeriya wato Global Peace Foundation, Rabaran John Hayad, ya bayyana yawan kawo addini a al’amarin da ya shafi kasa baki daya a matsayin rashin adalci. Ya kuma yi kira ga jama'a da su guji hanzarin yin hakan, ya na mai cewa rikicin da ya faru kwanakin baya a Najeriya kowa ya sani ba rikici ne na addini ba, wata dumuwar 'yan kasa ce da ake neman gyara.
Rikidewar zanga-zanga zuwa tarzoma a Najeriya ba sabon abu ba ne, an sha samun tarzomar addini da kabilaci a lokuta da dama sakamokon zanga-zanga ta lumana akan abin da ya shafi kasa.
Igwe Martins, dan kabilar Igbo ne, ya zargi 'yan siyasa da ruruta wutar rikici, ya na mai cewa babu kabilar da ba ta son zaman lafiya a Najeriya amma da zarar an bullo da wani abu mai kyau sai a kawo siyasa a ciki, shi ya sa ake da matsalar ci gaba a Najeriya.
Zanga-zangar ENDSARS ta kawo zargin juna a tsakanin manyan kabilun kasar abin da ya dada lalata makasudinta. Shugaban asalin 'yan birnin Abuja Danladi Jeji Oida, ya na ganin babu abun alherin da zargin juna zai kawo wa al’umma.
Ita ma Basarakiya Hajara Bello, Kilishin magajin garin Katsina, ta ce babu alherin da rikici da tarzoma zasu kawo a Najeriya, ya kamata jama'a su hada kai su daina barin baraka na shiga tsakaninsu.
Tun dai a ranar 8 ga watan Oktoban da ya gabata ne matasa a fadin Najeriya suka fara zanga-zangar neman a kawo karshen sashen rundunar ‘yan sanda na SARS, lamarin da ya rikide zuwa akasin makasudin shirya zanga-zangar da aka kai ga rasa rayuka da dukiyoyi.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5