Zamu Kalubalanci Hukumar NAHCON Domin Ta Damfari Alhazanmu - Gwamnan Jihar Neja

NAHCON - Hukumar Alhazan Najeriya

Bayan kammala aikin Hajjin bana na shekara ta 2023 a ranar jumma’a aka yi jifan shaidan na karshe, yanzu hankalin Alhazai ya karkata zuwa gida tare da duba nasarori da kuma matsalolin da aka samu a lokacin aikin Hajjin.

Jami’ar Labarai a hukumar Alhazan Najeriya, Fatima Sanda Usara, ta ce an samun kashi 95 na Alhazan Najeriya da suka ziyarci Madina kafin su iso Birnin Makka na daya daga cikin nasororin da aka samu.

Sai dai Gwamnan jihar Neja Alh. Umar Muhammed Bago, da ke cikin Alhazan Najeriya a aikin Hajjin na bana ya ce bai gamsu da inda aka sauke Alhazan jihar shi ba a zaman Mina don haka za su kalubalanci Hukumar Alhazai ta Najeriya.

Mina, Saudi Arabia

Amma hukumar Alhazan Najeriya ta ce matsalar ba daga wajanta bane inji Jami’ar Labarai a Hukumar Alhazan Fatima Sanda Usara.

Saudi Arabia Hajj

A gefe guda kuma jami’an kiwon lafiya na ci gaba da fadakar da Alhazai a kan kaucewa shiga ranar da ake kodawa a kasar ta Saudiyya tare da basu shawarwarin yawaita shan ruwa akai-akai.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Zamu Kalubalanci Hukumar Alhazan Nigeria Domin Ta Damfari Alhazanmu - Gwamnan Jihar Neja