Kwankwaso na magana ne yayin ganawa da wasu ‘yan majalisar dattawa na APC da su ka hada da Sanata Halliru Jika daga Bauchi da su ka sauya sheka zuwa NNPP.
Tsohon gwamnan na Kano wanda shi ma ya bar jam’iyyar APC da PDP ya dawo NNPP ya ce, barin wasu mutane ko jam’iyyu kalilan su na jan akalar dimokradiyyar Najeriya sabanin muradun al’umma, ya sa shi karfafa NNPP don zama zabi ga ‘yan siyasa masu ra’ayin sauya lamura.
Duk da Kwankwaso bai amsa tambayar tunanin da a ke yi kan cewa NNPP tamkar kadangaren bakin tulu ce, ya ce su na maraba da duk ga watan gobe.wanda zai zo a yi kawance don zaben mai zuwa.
Ku Duba Wannan Ma Hausawa Na Korafi Kan Rashin Ba Su Damar Neman Mukaman Siyasa A Jihar KwaraSanata Halliru Jika wanda tun farko ya mika wasika da aka gabatar a gaban majalisar dattawa ta ficewar sa daga APC zuwa NNPP, ya ce ya samu tikitin takarar gwamnan Bauchi kuma ba ya shakkar manyan jam’iyyun biyu.
Da ya ke sharhi, daya daga iyayen jam’iyyar Injiniya Buba Galadima ya ce jam’iyyar ta su na samun karbuwa da masu son takara kuma har ma sun cike dukkan guraben takarar.
Za a iya cewa zuwa yanzu ‘yan takarar gwamna a kusan dukkan jam’iyyu na duba hagu da dama, don sanin wadanda za su yi tafiya da su musamman ‘yan majalisar jiha gabanin mika sunayen ga hukumar zabe a ranar 15.
Saurari cilkken rahoton Hauwa Umar cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5