Barayin shanu a wasu yankunan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da cin karensu ba babbaka.
WASHINGTON D.C. —
Rahotanni sun ce satar shanun ta fi kamari a yankin garin Dan Sadau inda barayin suka kai hare-hare a kauyuka da dama dauke da manyan bindigogi.
Matsalar satar shanu na daga cikin manyan kalubalen da ke addabar hijar ta Zamfara inda makiyaya ke yin asarar dumbin dukiyoyi da ma rayukansu.
A jihohi irinsu Kano akan fuskanci wannan matsala ta shatar shanu , koda yake a farkon watan nan gwamnatin jihar ta yiwa wasu barayin shanu afuwa bayan da suka ce sun tuba.
Baya ga wannan matsala ta satar shanu, wani babban kalubale da makiyaya ke fusknata a Najeriya shi ne rikici tsakaninsu da manoma.
Saurari wannan rahoto na Murtala Faruk Sayinna domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5