An hana wa daya daga cikin yan adawan siyasar kasar Zimbabwe Tendai Biti mafakar siyar a kasar Zambia, jim kadan bayan da mahukuntar kasar ta Zimbabwe suka tsare shi lokacin da yayi kokarin tsallaka bakin iyaka.
Rahotanni farko sunce an kama shi.
Babban Darektan kungiyar nan ta kare hakkin bil Adama da ake kira Human Right Watch Dewa Mavhinga mai kula da kudancin Africa shine ya rubuta a shafin sa na twitter jiya laraba cewa ana sa ran kasar ta Zambia ta mayar da Biti shida wasu mutane 5 zuwa kasar ta Zimbabwe.
A cikin abinda ya rubutan har ya Ambato Biti yana cewa ga bisa dukkan alamu sun yanke shawarar mika mu ga gwamnati, mu dai muna hannun ALLAH.
Amma gidan radiyon BBC ko ya Ambato ministan harkokin wajen Zimbabwe Joe Malanji na cewa dalilan Biti na neman mafaka ba dalilai masu kwari ba, yace an ana kare Biti har sai ya dawo Zimbabwe.