Da alamu alamura sun soma daidaituwa a jihar Borno inda wasu kauyuka dake kewayen Maiduguri suka soma rayuwa irin na yau da kullum da suka saba yi kafin rikicin Boko Haram.
Muryar Amurka ta yi tattaki daga birnin Maiduguri zuwa wani kauye mai tazarar kilomita goma sha biyu daga babban birnin da ake kira Gongololowuntiri inda a ka ga jama'a da dama suna cigaba da walwala tare da gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.
Kauyen na cike da konannun gidaje da ma'aikatau da baraguzan makarantu da 'yan Boko Haram suka yi rugurugu dasu.
Cikin kauyen akwai mutane da dama da suka hada da mata da samari da kananan yara tare da nuna farin cikinsu da zaman lafiya da suka samu.
Amma sun jawo hankulan gwamnati dangane da matsalolin da suke fuskanta. Suna samun zaman lafiya amma basu da wutar lantarki ko kuma wadatacen ruwan sha. Suna kiran gwamnati ta kawo masu makarantu domin 'ya'yansu suna nan kara zube babu karatu. Sunna neman a yi masu asibiti a kuma basu jari domin su cigaba da sana'a.
A kan bukatun mutanen gwamnan Borno Ibrahim Kashim Shettima ya bayyana shirin gwamnatinsa. Yace zasu sake gina makarantun tare da ta kwanan yara. Zasu gina gidaje ishirin ishirin a kowane kauye da 'yan Boko Haram suka kona. Zasu kuma gina manya manyan makarantun firamare uku a mazabun sanatoci uku da jihar ke dasu. Akwai kudin kuma yanzu suna shirin bada kwangilar ginasu. Nan ba da dewa ba zasu fara gina azuzuwa 24 a kowane kauye.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5