Al'ummomin dake komawa Michika sun soma yin ramuwar gayya tsakaninsu bisa ga kabilanci da banbancin addini.
Yayin hare-haren da Boko Haram ta kai masu abubuwa da dama sun faru. Yanzu wasu suna zargin akwai hannun wasu a harin da aka kai masu lamarin da ya kaiga yiwa wasunsu kwantan bauna aka kashesu har lahira yayinda suke komawa gidajensu.
Wadanda aka kashen ana zargin wai addininsu daya da na 'yan Boko Haram. Haka ma an samu rahotanni dake cewa an bi wadanda suka kasa gudu lokacin da 'yan Boko Haram suka kai hari ana kashesu. Irin wannan ya faru a yankunan Michika, Madagali da Uba.
To saidai wasu shugabanni a yankunan Michika suna cewa dole a kai zuciya nesa idan ana son zaman lafiya ya tabbata a wurarensu.Mr Emmanuel Kwaci dan asalin garin Michika ya ziyarci ofishin Muryar Amurka inda yace babu wani mutumin Michika walau Kirista ko Musulmi da zai ce bai ji a jikinsa ba. Yace sabili da haka su rungumi juna. Su gafartawa juna. Su kaunaci juna. Yace ya kamata su zama mutane masu tunanen akwai gobe.Yace komi na iya faruwa amma Allah na nan zai kuma hukunta mutum.Ya kira duk mutanen Michika su kaunaci juna. Mantawa da abun da ya faru baya shi zai kaisu ga cigaba. Ramako zai jefasu cikin wata wahala daban.
Shi ma wani shugaban al'umma a yankin na Michika Alhaji Sadiq Umar shugaba a kungiyar musulunci da vigilante yace idan suna bukatar zaman lafiya dole ne su yi hakuri da juna. Su kawar da wasu banbance banbance. Yace shi musulmi ne amma kanisa kirista ne kuma fasto ne. Sabili da haka babu wata rabuwa da zasu yi.
A cikin gari ana zaman lafiya amma a gefen gari babu wanda ya isa ya je wurin. A gefen garin sai a ce kai musulmi ne dan kungiyar Boko Haram.
Haka ma an samu irin matsalolin a yankin Uba. Kamar yadda Danladi Dauda ya bayyana yace yayin da 'yan Boko Haram suka shiga karinsu sun cafke wani matashi da suka gani wanda 'yan Boko Haram suka suka tilasta masa ya nuna masu hanyar garin Tampul daga bisani suka sakeshi. To wadanda suka ganshi cikin motar 'yan ta'adan sun dauka shi ma yana cikinsu. Yanzu da ya koma sai wasu suka hallakashi.
Alhaji Abdullahi Damari yace akwai bukatar mayarda amincewa da juna kamarda. Gwamnati da masu hannu da shuni su tashi su taimakawa mutanen dake dawowa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz
Your browser doesn’t support HTML5