Hafsan Sojojin Najeriya, Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai, Ya ziyarci Sojojin Najeriya, dake faggen daga a jihohin Borno da Yobe, inda yace ziyarar tasa na ganewa ido ne da kuma yi masu alkawarin inganta kayan aiki da kuma sabbin dabaru na yadda za’a samu galaba kan ‘yan kungiyar Boko Haram.
Ya kuma kara da cewa zai tabbatar da ganin cewa sun samu kayayyakin more rayuwa domin samu damar gudanar da aikin su yadda yakamata. Manjo janar Burutai ya kuma bukaci jama’ar garin Kwanduga dasu koma gidajensu nada sati daya domin garin yanzu yana hannun Sojoji ne.
Ya kuma canja lakabin da akewa dakarun dake fafatawa da ‘yan Boko Haram, daga operation zaman Lafiya zuwa “Zaman Lafiya Dole” yace “ na farko anyi anyi a zauna lafiya dasu sun ki kullun muna zaune sai su kawo mana hari toh dole mu samu wani salo wanda za’a magance wannan tunda kowane dan Najeriya, na neman zaman lafiya,tunda su ‘yan Boko Haram, sun ce basu son zaman lafiya toh mu zamu kawo zaman lafiya dole Insha Allahu, kuma muna fatan cewa wannan canji zai karawa Sojojin karfin gwiwa.