Zainab ta ce tana da kimanin ma’aikata 20 da suke aiki a karkashinta. Ta kara da cewa kadan daga cikin kalubalen da suke fuskanta a cikin sana'ar mocktail shine yawan fasa musu kofuna, mussamam tunda tana amfani da kofinan tangaran. Sannan wadanda suka gayyace su biki basa biya idan an fasa musu kofinan.
Ta ce abin da ya ja mata hankali ta fara wannan sana’a, shine sakamakon ita ma’abociyar kayan marmari ce. Domin haka sai ta lura da cewar amfani da kayan marmari wata hanya ce ta samun kudade, kuma sana’a ce ba tare da neman jari ba.
Ta kara cewa hakan kuwa ya faru ne a wani biki da ta je inda aka bukaci abin sha, sai ta bada shawarar, me zai hana ayi amfani da kayan marmari wajen samar da lemo, kamar yadda turawa ke yi. Bayan ta hada lemon, sai ta samu yabo mai yawa daga wajen mutane.
Zainab ta ce babban burin ta bai wuce ta bude babban shagon mocktail ba wanda zai yi shahara a Najeriya.
Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5